🧾 LABARAN TARIHI 🧾

Barka da zuwa shafin Labaran Tarihi!

Mun ƙirƙiri wannan channel ne domin kawo muku Labaran Tarihi Na Gaskiya, masu ma’ana da ƙayatarwa waɗanda ke faɗakarwa, ilmantarwa, da nishaɗi.

📌 Ku kasance tare da mu domin karɓar ilimi, hikima, da tarihin rayuwa — cikin sauƙi da salo.


LABARAN TARIHI

MUNA ROƘON LIKE NA VIDEOS NAMU..🙏🙏
••••••••••••••••••••
∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆
~~~~~~~~~~~
Muna Qara Godiya Ga Ƴan Uwa Masu Bibiyarmu Akoda yaushe Kuma Suke Bamu Goyon baya 100% MUNGODE.

ALFARMA.........🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏

Asatinnan Munyi Videos 2 Na Tarihin Annabi Yunus (As), Video Na Farko Yasamu Views 1.5k Amma Likes (79) yasamu 😭😭

Shikuma video na Biyu Yasamu Views 409 Amma Likes 31 ne yasamu 😭😭

Bawai Saboda kun Gazaba Kokuma Qorafi A'a wannan Neman Alfarma ne muke Agareku Dan Allah Kudinga Yin Like Na videos namu aduk lokacin da kuke kallonsu ko kuma kukaci karo dasu MUNA ROƘO.

TASHAR LABARAN TARIHI ZATA KASANCE TAREDAKU INSHA ALLAH A KODA YAUSHE.

MUNGODE.

1 month ago | [YT] | 56

LABARAN TARIHI

♦️GODIYA TA TABBATA GA ALLAH♦️

Insha Allah Yau Zamu Ɗora Video Na Qarshe Na Tarihin Annabi Musa (As) 😭.

Sannan Zamu Cigaba Da Tarihin Annabi Yusha'u (As)

9 months ago | [YT] | 40

LABARAN TARIHI

ALHAMDULILLAH................
💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠

Kamar yadda Muka Saba A'kowane Sati Muna Saka Videos Guda 3.

Laraba ✅
Juma'a ✅
Lahadi ✅

Yanzu Muka Saka Videon Mu Na Qarshe A wannan Satin, Ga Link Idan Baka Kalla Ba 👇

https://youtu.be/J91RFatxeaY?si=VCMF8...

Har Yanzu Dai Muna Cikin Tarihin Annabi Yusuf (As) Insha Allah Ranar Laraba Idan Allah Ya Yarda Ya Kaimu Zamu Cigaba,

Ku Kasance Tare Damu kuma Kuyi Subscribe, Like, Share

MUNGODE 🙏🙏🙏🥰🥰🥰♥️♥️♥️

10 months ago (edited) | [YT] | 11

LABARAN TARIHI

Yaya Kukeso Mudinga Ɗora Vidios namu??

11 months ago | [YT] | 40

LABARAN TARIHI

Kuzaɓi Ranakun Dakukeso Mudinga Ɗora Muku Videos Namu Cikin kowane Sati 👇👇

11 months ago | [YT] | 40

LABARAN TARIHI

Shin Kuna Buƙatar Videos Namu Su dinga Tsawo

Kuzabi Daya Daga cikin Wannan Zabin 👇👇

11 months ago | [YT] | 38

LABARAN TARIHI

TARIHIN LARABAWA KAFIN ZUWAN MUSULUNCI

Sashe na 1: Halin Duniya da Larabawa a Jahiliyya
Kafin zuwan Musulunci, duniya gaba ɗaya tana cikin wani irin duhu na zalunci da bautar gumaka. Babban abin da ya fi bayyana wannan zamani shi ne, kowace al’umma ta yi nisa daga gaskiya, ta dogara da gumaka kokuma wani abin bauta da ba shi da tushe.

1. Yadda Duniya Take Alokacin
A gabashin duniya akwai Fārisawa (Persiya). Su sun dogara da bautar wuta. Sunada mulki mai ƙarfi, amma zalunci da rashin adalci sun mamaye shi.

A yamma akwai Rumawa (Byzantines). Sun riƙe Kiristanci, amma sun gauraya shi da siyasa da zalunci. Sarakunan su suna zaluntar jama’a, kuma tsananin rarrabuwa ya shiga cikin addininsu.

A kudu akwai Habasha (Abyssinia). Su ma suna da Kiristanci, amma sun kasu kashi-kashi. Sun dogara da karfin mulki da zalunci.

A arewa akwai Yahudawa a wurare daban-daban, amma addininsu ya lalace, ya cika da son zuciya da wariya.

Dukkan waɗannan suna nuna cewa duniya gaba ɗaya tana bukatar wani sabon tsari na gaskiya da adalci.

2. Larabawa a Hamada

Larabawa suna cikin hamadar Hijaz, Najd da Yemen. Rayuwarsu ta kasu gida biyu:

Larabawan gari: waɗanda ke zaune a birane irin su Makka, Yathrib (Madina), da Yemen. Su kan yi kasuwanci, musamman a Makka, inda ake gudanar da cinikayya tsakanin gabas da yamma.

Larabawan hamada (baduwa): su ne ke yawon kiwo da rakuma da awaki. Su kan yi rayuwa mai tsananin wahala saboda hamada mai zafi da ƙunci.

Babu shugaba guda a kan su gaba ɗaya. Kowace ƙabila tana da nata shugabanta, kuma ƙabilanci ne ke jagorantar rayuwarsu. Wannan ya haifar da yaƙe-yaƙe da rikice-rikice tsakanin kabilu, wanda ake kira ayyāmu-l-‘Arab (yaƙe-yaƙen Larabawa).

3. Addini Addinin Larabawa
Larabawa sun gaji Ka’aba daga Annabi Ibrahim (AS), amma daga baya suka cika ta da gumaka sama da gumaka 360. Kowace ƙabila tana da gumakanta. Suna yin sujada ga duwatsu da itatuwa, suna kiran su "ubangiji". A lokacin hajji sukan yi ɗawafi da Ka’aba, amma suna faɗin kalmomin shirka.

Baya ga bautar gumaka, akwai:
Kiristoci a Yemen da wasu garuruwa.
Yahudawa a Madina da Khaibar.

Kuma akwai wasu mutane da ake kira hunafā’u, waɗanda suka ƙi bautar gumaka, suna neman gaskiya, suna cewa Allah guda ɗaya ne kawai.

4. Zamantakewa

Rayuwar zamantakewar Larabawa ta dogara da ƙabilanci. Kowa yana alfahari da asalinsa da nasabarsa. Girmamawa tana zuwa ne bisa ga ƙabilar mutum, ba bisa gaskiya ko adalci ba.

Mata a wannan lokaci ba su da daraja. A wasu ƙabilu, idan aka haifi mace, uba zai binne ta da ranta domin gujewa abin da suka kira kunya. A wasu wurare, mace tana a matsayin abin mallaka.

Bayin kasuwa suna da yawa. Ana saye da sayar da su a kasuwanni. Ana ɗaukar su tamkar kaya, ba mutane ba.

5. Tattalin Arziki

Tattalin arzikin Larabawa ya ta’allaka ne akan:

Kiwo da rakuma a wajen badawa.

Kasuwanci a birane, musamman Makka. Kasuwanni irin su Suuq Ukaz sun kasance shahara.

Yawon hajji ya zama wata hanyar samun kuɗi, saboda jama’a daga wurare daban-daban sukan zo Makka.

Wannan duk yana nuna cewa Larabawa suna cikin duhu na jahiliyya. Babu adalci, babu tsari nagari. Duk duniya tana jiran sabon haske, sabon tsarin da zai gyara halin mutane. Wannan shi ne yanayin da Musulunci zai bayyana daga ciki.

1 year ago | [YT] | 24